Uganda: Sabon salon daukar hotunan bidiyo | Himma dai Matasa | DW | 12.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Uganda: Sabon salon daukar hotunan bidiyo

Wani matashi  a Uganda mai suna Asaph Kasujja ya yi fice wajen iya sarrafa jirgi maras matuki wanda ya ke amfani da shi wajen daukar fina-finai da yin fayafayen bidiyo na mawaka da makada ko kuma daukar manyan taruka.

Shi dai wannan matashi ya zabi yin amfani da jirgi maras matuki ne wajen daukar hotuna na bidiyo ko kuma irin abinda ya ke wakana a wuraren da ake gudanar da manyan takura wanda ba kasafai aka saba gani ba a kasar. Matashin ya ce nan gaba ma fatansa shi ne ya zama matukin jirgi na gaske.

Matashin dai ya fara wannan aiki ne bayan da gaza samun kudin da zai yi amfani da su wajen cigaba da karatunsa bayan da ya kammala karatun sakandare inda ya ce a wannan lokacin ''zabi biyu ya rage min, ko dai in shiga aikin soja ko kuma in shiga makarantar koyan tukin jirgi. To amma ta na da tsananin tsada kuma iyaye na ba su da wadatar iya biya min dan haka na kama wannan hanya ta daukar fayafayin bidiyo"

A shekara ta 2012 ne a karo na farko Asaph da abokin huldarsa suka taba ganin jirgin marar matuki da ake kira drone a cikin talabijin, kuma nan take suka fahimci cewa za su iya amfani da shi a cikin aikin daukar fina-finan bidiyo da suke yi. Daga na sai suka hada kudi dala 800 suka yi odar jirgin maras matuki sai suka nemi wani da ya iya sarrafa jirgin suka biya shi ya koya masu suma kuma ba tare da bata lokaci ba suka soma aiki da shi. Yanzu dai kasuwar daukar bidiyo da jirginmarar matuki ta Asaph Kasujja ta habaka sosai a kasar ta Uganda inda ya zamo tamkar wani kwararre da ke koyar da tukin jirgin a tarin 'yan kasar.