1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala ginin filin jirgin saman Istanbul

Zulaiha Abubakar
October 29, 2018

Shirye-shirye sun yi nisa don bude katafaren filin jirgin saman kasar Turkiyya wanda shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan zai yi a wannan Litinin a ci gaba da bukukuwan cikar kasar shekaru 95 a matsayin Jamhuriya.

https://p.dw.com/p/37KFH
Istanbul Einweihung neuer Flughafen
Hoto: Reuters/M. Sezer

Sabon fili jirgin saman dai na da hanyoyin saukar jirage har guda uku bayan tanadin masaukan fasinjojin da yawansu zai kai miliyan casa'in,ana sa ran jirgi zai fara tashi daga filin jirgin a ranar Larabar wannan makon.

Sai dai kungiyar ma'aikatan kamfanin da yayi aikin ginin filin jirgin ta zargi jagororin kamfanin da yin watsi da bukatun su bayan wata zanga-zanga da suka gudanar don neman a karin albashi lamarin da ya sanya jami'an tsaro suka kame sama da mutane 37 wadanda kuma har yanzu suna garkame a gidan yari.