Turkiyya ta kama wani jirgin Kasar Rasha da ya keta ta sararin samaniyar ta. | Labarai | DW | 05.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiyya ta kama wani jirgin Kasar Rasha da ya keta ta sararin samaniyar ta.

Turkiyya ta bayyana cewar wani jirgin ta mai suna F16 ya sami nasarar dakatar da wani jirgin yakin saman Rasha wanda ya keta sararin samaniyar ta a kusa da kan iyakar Siriya tare da tilasta wa jirgin komawa da baya.

Ta cikin sanarwar data fitar mahukuntan Turkiyyan sun gayyaci jakadan Rasha dake a birnin Ankara zuwa ma’aikatar harkokin wajen Turkiyan a inda suka nuna rashin jin dadin su kan kutsen da jirgin Rashan yayi a sararin samaniyar kasar.

Sanarwar ta kara da cewar muddin aka kara kwatawa to Rashan baza taji da dadi ba.

Tun dai a ranar asabar din nan ce jirgin Rashan yayi kutse a sararin samaniyar Turkiya da misalign karfe 9 a gogon GMT a kudancin lardin Yayladagi ata cewar ma’aikatar harkokin wajen Turkiyyan.

Tuni dai ministan harkokin wajen Turkiyan ya kira takwaran san na Rasha Sergei Lavrov don nanata masa damuwar mahukuntan kasar kan kutsan jirgin na Rasha.