1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya: Janye kariya ga wasu Jakadu 10

October 23, 2021

Shugaban kasar Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya ce za a janye duk wata kariya da ake baiwa jakadu 10 da suka nemi a saki dan fafutukar na kasar Osman Kavala.

https://p.dw.com/p/426QU
Ankara Parlament Sondersitzung Putsch Jahrestag Erdogan
Hoto: picture-alliance/AA/E. Aydin

Ana dai ganin hakan a matsayin wata alama ce da ke nuna matakin farko kafin korarsu. Sai dai har kawo yanzu shugaba Erdogan bai baiyana karara ko matakin nasa na nufin jami'an diflomasiyyar da ake zargi da taurin kai za su bar kasarsa ba.

Tun dai a ranar Talatar data gabata ce dai ministan harkokin wajen Turkiyya ya gayyaci jakadun kan kalamansu da ya baiyana a matsayin mara tushe. Jakadun dai sun tura da sakon hadin gwiwar da ba kasafai ake samun irinsa ba, suna neman a gaggauta sakin dan fafutukar da ake tsare da shi na tsawon shekaru hudu. Daga cikin Jakadun da za su fuskanci wannan hukunci har da na kasashen Amirka da Jamus da Kanada da kuma Sweden.

Tun dai a watan Satumbar da ya gabata ne dai kotun kare hakkin bil adama ta Turai ta yi gargadin karshe ga Turkiyya kan ta saki Kavalan mai shekaru 64 ko kuma ta fara shari'ar cin zarafin dan adam da gwamnatin kasar nan da karshen watan Nuwamba mai kamawa.