Turkiyya ta ba da umarnin kame ′yan jarida masu sukar gwamnati | Labarai | DW | 25.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiyya ta ba da umarnin kame 'yan jarida masu sukar gwamnati

Fiye da mutane dubu 13 ke hannu sannan kimanin 6000 na daure tun bayan yunkurin juyin mulkin na ranar 15 ga watan nan na Yuli.

Türkei Präsident Recep Erdogan Yildirim Akar

Recep Erdogan a tsakiya da Firaminista Binali Yildirim a hagu sai Hafsan soji Janar Hulusi Akar

Bayan ayyana dokar ta-baci a kasar Turkiyya, lauyoyin gwamnati a birnin Santambul sun ba da sammacin kame 'yan jarida 42 ciki har da daya daga cikin sanannun masu sukar lamirin gwamnati. Kamfanin dillancin labarun kasa, Anadolu ya ce 'yar jarida Nazli Ilicak na daga cikin 'yan jaridu 42 da ake zargi a binciken da ake yi kan masu hannu da yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba. Sai dai kamfanin dillancin labarun DHA ya rawaito cewa binciken ya ta'allaka ne kan kafofin yada labaru masu nasaba da malamin nan mai wa'azi Fethullah Gülen, wanda gwamnatin Turkiyyar ta dora wa laifin yunkurin juyin mulkin. Fiye da mutane dubu 13 ke hannu sannan kimanin 6000 na daure tun bayan yunkurin juyin mulkin na ranar 15 ga watan nan na Yuli.