Turkiyya: Binciken harin ta′addanci a Ankara | Labarai | DW | 18.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiyya: Binciken harin ta'addanci a Ankara

Hukumomin kasar Turkiyya sun lashi takobin yin martani dangane da abun da suka ce harin ta'addanci a birnin Ankara, wanda ya yi sanadiyyar rayuka tare da raunata wasu.

Akalla mutane 28 aka kashe a birnin Ankara na kasar Turkiyya lokacin da wata mota makare da bama-bamai ta yi bindiga lokacin da motocin bas na sojoji ke jiran denja ta ba su hanya a tsakiyar babban birnin kasar ta Turkiyya.

Ofishin gwamnan birnin ya ce an kai harin ne kusa da gine-ginen gwamnati da shalkwatar soji. Mukaddashin Firaminista Bekir Bozdag ya ce hari ne na ta'addanci.

A kuma halin da ake ciki Firaminista Ahmet Davutoglu ya soke tafiyar da so yi zuwa birnin Brussels. A wasu tagwayen hare-hare da aka kai birnin cikin watan Oktoban 2015 fiye da mutane 100 suka hallaka.