Turkiya ta sake kira ga Amirka ta mika mata Gülen | Labarai | DW | 25.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya ta sake kira ga Amirka ta mika mata Gülen

Gwamnatin Turkiya ta sake sanya kira ga Amirka da ta mika mata babban malamin nan Fetullah Gülen wanda take zargi da kitsa juyin mulkin da ya ci tura a watan Yulin da ya gabata a kasar. 


Gwamnatin Turkiya ta sake sanya kira ga Amirka da ta mika mata babban malamin nan Fetullah Gülen wanda take zargi da kitsa juyin mulkin da ya ci tura a watan Yulin da ya gabata a kasar.Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Turkiyar na Anadolu ne ya ruwaito wannan labari a wannan Talata inda ya ce ministan ma'aikatar shari'a na kasar ta Turkiya Bekir Bozdag ya jaddada wannan kira a dai dai lokacin da yake shirin tashi zuwa kasar ta Amirka inda zai gana da takwarsa Loretta Lynch. Ministan ma'aikatar shari'ar kasar ta Turkiya ya bayyana cewaR kin mika masu Güllen abu ne da ka iya yin illa ga huldar diplomasiyyar kasashen biyu.