1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta salami wakilin kungiyar RSF

Abdourahamane Hassane
July 17, 2019

Wata kotun a Turkiya ta salami wakilin kungiyar 'yan jaridu na kasa da kasa Reporters Sans Frontières Erol Önderoglu wanda ake zargi da yin farfagandar ta'addanci tare da hadin kan wata jaridar ta kusa da Kurdawa.

https://p.dw.com/p/3MDMJ
Erol Onderoglu bei Pressekonferenz
Hoto: Getty Images/AFP/O. Kose

Wata kotun a Turkiya ta salami wakilin kungiyar 'yan jaridu na kasa da kasa Reporters Sans Frontières Erol Önderoglu wanda ake zargi da yin farfagandar ta'addanci tare da hadin kan wata jaridar ta kusa da Kurdawa. Onderoglu wanda aka kamasu su uku aka tsare tun a shekara ta 2016 kafin daga bisani a yi masa daurin talala, ya ketare rijiya da baya ga hukuncin da ya ka iya fuskanta na daurin shekaru 14 na zaman gidan yari idan da a sameshi da laifi.