1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya: An cafke wanda ake zargi da kai harin Santanbul

Salissou Boukari
January 17, 2017

Bayan wani binciken kwakwaf a wata unguwa ta birnin Santanbul, 'yan sandan kasar Turkiya sun cafke mutumen da ake zargi da kai harin da ya kashe mutane 39 a jajibirin shiga sabuwar shekara.

https://p.dw.com/p/2VtmB
Istanbul Türkei mutmaßlicher Terrorist verhaftet
'Yan sandan Turkiya yayin da suke kokarin kama wanda ake zargi da kai hariHoto: picture alliance/AA/A.Coskun

A cewar kanfanin dillancin labaran kasar ta Turkiya na Anadolu, wanda ake tuhumar sunan shi Abdulgadir Masharipov, sai dai kuma a cewar kanfanin dillancin labarai na Dogan mutumen na amfani da sunan Abou Mohammad Khorassani a matsayin sunansa na badda sawu a cikin kungiyar IS.

Shi dai Abdulgadir Masharipov mai shekaru 34 da haihuwa, an kamashi ne ya yin da yake tare da dansa mai shekaru hudu a wata Unguwa ta birnin Santanbul bayan da aka gudanar da wani babban binciken 'yan sanda a cewar tashar talbijin ta kasar ta TRT. Tun dai da kwanaki uku ne 'yan sanda na Turkiya suka gano maboyarsa, amma kuma suka yi ta bin shi domin gano abokan tafiyarsa.