Turai za ta tallafawa Yukren | Siyasa | DW | 24.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Turai za ta tallafawa Yukren

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ƙudiri aniyar taimakawa ƙasar Yukren da milliyoyin euro, kuma babbar kantomar dake kula da harkokin wajen ƙungiyar Catherin Ashton na Kiev domin tattauna ƙa'idojin bayar da waɗannan kuɗade

Amirka da Asusun bada Lamuni na Duniya wato IMF da ma Rasha na sa ran ba da na su gudunmawar amma kuma har yanzu ba a kai ga tantance hanyoyin da za a bi dan cimma wannan buri ba.

Babbar kantomar kula da harkokin wajen Turan Catherine Ashton, ta tafi ƙasar Yukren ɗin ne domin tattaunawa da sabbin jagororin ƙasar kan tallafi kuma ta bayyana cewa tana da guzurin tallafi na ƙasa da ƙasa wanda zai taimakawa Yukren, a gajeren lokaci, da matsakaicin lokaci da kuma dogon lokaci domin ta samu ta tayar da komaɗar tattalin arziƙinta To sai dai abin da take musu tayi da ma yawan kuɗin da zasu bayar ba wanda ya sani.

Kafin tafiyar na ta Catherine Ashton ta yi kira ga ɓangarorin na Yukren da su mutunta demokraɗiyya, da 'yancin kai da cikakken ikon da ƙasar ke da shi

Matsayin Turai a taron ministocin kuɗin G20

Europaabgeornete Rebecca Harms

Rebecca Harms, 'yar majalisa a Majalisar dokokin Turai

A taron da ministocin kuɗin ƙasashe 20 masu ƙarfin tattalin arziƙi suka gudanar ranar lahadi a birnin Sydney na ƙasar Australia, Kwamishanan kula da harkokin tattalin arziƙin Tarayyar Turai Olli Rehn ya ce a yanzu dai kudin da za su baiwa Yukren sai billoyi domin ya wuce ɗaruruwa.

Ko a lokacin da rikicin siyasar ƙasar ya yi ƙamari ƙungiyar ta yi ta nanata cewa yarjejeniyar ma'amala da kasuwanci mara shinge na nan kuma suna iya sanya hannu a duk lokacin da suka shirya amma komai yana hannun Yukren.

A ƙarshen makon da ya gabata, Jagorar 'yan jami'yyar The Greens masu manufofin kare muhalli a Majalisar dokokin Turai Rebecca Harms bayan da ta gana da tsohuwar Firaministar ƙasar Julia Tymoshenko, ta faɗawa DW cewa wajibi Turai ta hanzarta wajen ƙulla guzurin tallafin

EU Außenminister Treffen zur Ukraine 20.02.2014 Brüssel Ashton

Catherine Ashton

Yunƙurin samun tallafin IMF da farko ya ci tura

A bara dai tattaunawar da Yukren ta yi da Asusun bada Lamuni na duniya domin ƙulla yarjejeniyar samun bashi ta wargaje domin sun gaza amincewa da wasu sharuɗɗa to amma 'yar siyasar ta Turai ta ce ba kamata a ce an sake samun wata tangarɗa ba

"Bai dace a ce Asusun bada Lamuni ta duniyar tana dogara da tsoffin sharuɗɗanta ba, ya kamata a lokaci guda a yi fatan cewa komai ya zo ƙarshe domin mafi yawan arziƙin wannan ƙasa na fita waje ne domin ba'a zuba jari, kuma ana gudun biyan haraji ga kuma wanke haramtattun kuɗaɗe. Idan har aka shawo kan wannan, za a yi nasarar samun kuɗi zubawa a cikin ƙasa"

To sai dai shugabar Asusun Christine Legard ta riga ta bayyana cewa kafin Yukren ta sami wani tallafi daga wurinta, sai ta gudanar da aƙalla wasu sauye-sauye a fanin kuɗaɗenta, kuma ma ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmaier ya ce a cikin wannan makon shi da kan sa zai tattauna batun bashin na Yukren da asusun na IMF

Shawarar 'yan siyasan Ukraine

Ukraine Julia Timoschenko freigelassen 22. Feb. 2014

'Yar adawa Julia Tymoschenko

Wanda ke riƙe da muƙamin ministan kuɗi na riƙo Juri Kolobow ya yi tayin cewa Kiev ta gudanar da taron ƙoli na masu ba da tallafi, inda ya bayyana buƙatar ƙasar ta aƙalla euro milliyan dubu 25, ƙungiyoyin dake auna ƙarfin tattalin arziƙin ƙasashen duniya na ganin cewa Yukren ba zata iya biyan kuɗin ba domin tattalin arzƙinta na dab da durƙushewa. Wakilin gabashin Turai da Rasha a gwamnatin Jamus ya ce Rasha za ta baiwa Yukren tallafi tun da dama ko lokacin da Yanukovich ke nan, ta bayar da dala Milliyan biyu

"Yana ba da shawarar shiga tattunawa da Rasha, domin ita ma Rashar tana buƙatar ganin cewa abubuwa ba su lalace ba, illa ma a koma a sami daidaito, wato maƙociyar ta zauna cikin kwanciyar hankali, babu shakka Rasha ta na da wannan buri"

Har yanzu dai Tarayyar Turai tana barazanar ƙaƙaba takunkumi kan duk wani ɗan siyasa ko ɗan kasuwa dake da hannu a rikicin na Yukren wanda ya kai ga hallakar jama'a.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin