Tumbatsar kogi na barazana ga Tsibirin Goree | Zamantakewa | DW | 20.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Tumbatsar kogi na barazana ga Tsibirin Goree

Tsibirin Gorée dake gabar ruwan Senegal, ya kasance wuri mai dunbin tarihi wanda hukumar UNESCO ta aminta da shi tun shekarar 1978 kuma irinsa na farko a nahiyar Afrika na fuskantar barazanar sauyin yanayi

Tsibirin Gorée, wani karamin tsibiri ne a gabar ruwan Senegal, ya kasance wuri mai dinbin tarihi na ajiye kayayyakin tarihi wanda hukumar UNESCO ta aminta da su tun shekarar 1978 kuma shi ne irinsa na farko a nahiyar ta Afrika.

Sai dai yanzu matsalar sauyin yanayi da tunbatsar teku na barazana ga wannan wuri, amman kuma Hukumar raya ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta UNESCO ta dauki mataki don kare kayyakin tarihin da ke tsibirin na Goree.

Senegal Goree Island (picture alliance/AP Photo/N. Evatt)

Hoton tsibirin Goree a kasar Senegal

Zuwa tsibirin Goree tafiya ce ta mintuna 20 kacal da kwalekwale daga Dakar babban birnin kasar, babu ababen hawa da ka iya janyo cikas ga jin dadin masu yawon bude a wannan tsibirin da ke da dunbin tarihi. An fara samun matsala kan kare tsibirin a sakamakon ruwan sama mai karfi shekaru biyu da suka gabata a wannan tsibiri da ke karbar bakuncin masu yawon bude ido kusan dubu dari biyu a kowacce shekara, Hukumar raya ilimi da al'adu UNESCO ta baiyana girman lamarin sai dai duk da wannan barazana, jama'a na ci gaba da sintiri, Emilie mai shekaru hamsin ta ce duk da wannan barazana ba ta fargaba ko kadan.


"Sam bama fargaba amma dai lamarin na da hadarin gaske''
Daga karni na goma sha biyar zuwa sha tara an kiyasta cewa 'yan Afrika miliyan ashirin ne suka bi ta tsibirin da ke zama zangon safarar bayi daga Afrika a wancan lokaci, dubban mutane na zuwa Goree domin shaida abinda ya faru duk kuwa da barazanar da ya ke fuskanta, a shekarun baya bayan nan Emilie ta ce a kan idanunta ruwa ya kwashe wasu masalatai da ke gabar tsibirin.


Senegal Goree Island (imago/F. Stark)

Kogi na neman cimma gidaje a tsirinn Goree

"lamarin ya auku da rana tsaka, gaskiya akwai bukatar mahukunta su dauki mataki don komai da ke gabar ruwan ya lalace, abin babu kyau''
 

Wani mazaunin yankin Imam Baila limamin wani massalaci a tsibirin ya nemi a dauki kwararran matakai don kauce wa abinda ka iya biyo baya.

''Dole a kyautata tsaro da bai wa kwararru damar kulawa da tsibirin Goree, ina matukar fargabar yadda barazanar da muke fuskanta a sanadiyar tunbatsar teku da mu kanmu ke ciki''  


Za a iya shawo kan matsalar duk da cewa UNESCO ta gudanar da wasu ayyuka na gyara tsibirin a can baya, an kiyasta cewa ana bukatar kudi akalla yuro miliyan arba'in don aiwatar da sabbin gyare-gyare a tsibirin na Goree.

Sauti da bidiyo akan labarin