Tsugune ta ki karewa a Masar | Labarai | DW | 24.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsugune ta ki karewa a Masar

Wani harin Bom da aka kai a kasar Masar ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 14 tare kuma da jikkata wasu da dama.

Kakakin gwamnatin wucin gadi ta kasar Sherief Shawki, ya dora alhakin harin da aka kai da mota a ofishin 'yan sanda na kasar kan kungiyar 'yan uwa Musulmi dake ci gaba da zanga-zanagar nuna adawa da kifar da gwamnatin Mohamed Morsi.

Mahukuntan kasar ta Masar dai sun bayyana harin da aka kai da sanyin safiyar wannan Talatar (24.12.13) da wani yunkuri na dakile kokarin gwamnati na komawa kan turbar dimokaradiyya a kasar. Rahotannin sun bayyana cewa sa'oi kalilan bayan kai harin, Firaministan kasar Hazem Beblawi ya sanya kungiyar 'yan uwa Musulmi dake goyon bayan hambararren tsohon shugaban kasar Mohamed Morsi a sahun kungiyoyin ta'adda.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Saleh Umar Saleh