1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsugune ba ta kare ba ga ma’aikatan Amirka

January 9, 2019

Murna ta koma ciki ga dubban ma’aikatan gwamnatin Amirka cewa za a gaugauta kawo karshen takun-saka tsakanin Shugaba Trump da majalisar dokoki kan samar da kudin gina shingen tsaron iyakar kasa da rashin biyan su albashi

https://p.dw.com/p/3BGE0
Präsident Trump spricht vom Oval Office aus die Nation zur Grenzsicherheit an
Hoto: Getty Images/C. Barria-Pool

Fiye da makonni biyu kenan al'amura suka tsaya cak a wasu ma'aikatun gwamnatin Amirka sakamakon sabanin da ya haddasa takaita wasu ayyukan, da kuma rashin biyan albashi. Wannan sabani ya kara tabbata ne cikin jawaban baya-bayan nan da Shugaba Trump da shugabannin adawa na Demokrats suka yi wa kasa, inda kowannensu ya sake jaddada dalilansa na goyon da kuma adawa da kashe dala kusan bilyan 6 dan gina wannan Katanga. Shugaba Trump ya bayyana matsalar tudadowar bakin haure daga kudancin kasar a matsayin wata babbar damuwa. Ya ce idan aka yi la’akari da yawancin kashe-kashe, da safarar kwayoyi, haramtattun ‘yan-cirani ne suka fi aikatawa a cikin kasa,

Mexiko Tijuana Migranten hinter dem Grenzzaun in den USA
Iyaka tsakanin Amirka da MexicoHoto: Getty Images/AFP/G. Aras

"Ana kashe fiye da dala bilyan 500 wajen harkar muggan kwayoyi kowace shekara a kasar nan, adadin ya zarta nesa ba kusa ba, dala biyan 5 da milyan 700 da muka bukata daga majalisa".

Shugaban na Amirka ya ce, wannan wani zabi ne tsakanin abin da ya dace da wanda bai dace ba, rarrabewa ce a tsakanin adalci da rashin adalci. Haka kuma Sabanin hasashen da aka yi, Shugaban na Amirka bai ayyana kafa dokar ta baci ba, wadda zai iya yin amfani da ita wajen cimma burinsa ba tare da majalisa ba. 

Ina Kira ga kowane Dan majlisa, ya zartar da kudirin da zai kawo karshen wannan rikici. Ga kowane Dan kasa, ku yi kira ga ‘yan majalisa, su tabbatar da tsaron iyakarmu bayan shekaru da aka shafe.

Washington Kongress konstituierende Sitzung Pelosi
Nancy Pelosi shugabar majalisar wakilan AmirkaHoto: picture-alliance/dpa/J. L. Magana

Da suke mayar da martani, ‘yan jam’iyar adawa ta Demokrats a ta bakin shugabar majalisar dokoki Nancy Pelosi da Sanata Chuck Schumer, sun yi kokarin nuna wa jama’a cewa, bayanan Trump cike suke da kurakurai, inda ya yi kokarin ci gaba da tsorata Amirkawa maimakon fadin gaskiyar lamari.

Nancy Pelosi ta ce "gaskiyar magana ita ce, a ranar farko ta wannan sabuwar majalisar ‘yan Demokrats sun zartar da wani kudirin majalisar dattawa ta Republican, wanda ya tanadi sake komawa aikin gwamnati gadan-gadan, sannan a samar da kudin inganta tsaron iyaka da suka fi dacewa, amma sai Shugaban kasa yayi fatali da kudirin."

'Yan majalisar dokokin na jam'iyyar Demokrats sun kuma musanta zargin da Trump yayi cewa suna sakaci da tsaron kasa, suna masu cewa, mata da yara masu neman mafaka a Amirka ba wata barazana ba ce ga tsaron kasar.