Tsugune ba ta kare ba a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 10.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsugune ba ta kare ba a Sudan ta Kudu

'Yan tawaye a Sudan ta Kudu sun yi barin wuta a yankin da dakarun sojan kasar suka ja daga a garin Bentiu mai arzikin albarkatun man fetir.

Wannan kuma na zuwa ne kwana daya bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da asusun neman tallafin sama da miliyan dubu daya da za a yi amfani da su dan tallafa wa kasar da ta samu kanta a cikin yanayi na yunwa wacce kuma tuni ke ciki yanyi na yaki.

An dai ji karar ababan fashewa a arewacin garin na Bentiu da ke zama fadar gwamnatin Jihar Unity garin da ke kan gaba-gaba wajen samun kai a yanyi na halin kaka na kayi cikin yaki da kasar ta fada na watanni goma sha hudu , wurin kuma da fararen hula 53, 000 ke neman mafaka a sansanonin Majalisar Dinkin Duniya.

Kuol Manyang ministan harkokin tsaro na kasar ta Sudan ta Kudu ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa wannan farmaki da aka kai musu wani bangare ne na keta yarjejeniyar zaman lafiya da ake kullawa kuma suma a nasu bangaren a shirye suke su mayar da martani.

Kimanin mutane miliyan biyu ne aka tilasta musu kaurace wa muhallansu inda kimanin 500,000 suka tsallake zuwa kasashe makota kuma 50,000 suka halaka a cewar kungiyoyin kasa da kasa da ke sanya idanu a kan rikice-rikice.