1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniAfirka

Tsohon zakaran duniya Anthony Joshua ya doke Francis Ngannou

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 9, 2024

A dambensa na farko dai sauran kiris ya samu nasarar doke zakaran duniya Tyson Furry bayan ya kai shi kasa

https://p.dw.com/p/4dKeZ
Hoto: Nick Potts/PA/picture alliance

Tsohon zakaran damben duniya Anthony Joshua ya doke abokin karawarsa Francis Ngannou na Kamaru, a fafatawar da suka yi a Kingdom Arena da ke birnin Riyadh na kasar Saudi Arebiya a daren Juma'a.

Karin bayani:Wasanni: Damben boxing da wasan guje-guje da kwallon kafa

Bayan gwabzawar ne sai suka rungumi juna inda suka tattauna. Daga bisani Anthony Joshua ya shaidawa 'yan jarida cewa ya shawarci Francis Ngannou da ya ci gaba da damben domin akwai alamun nasara a nan gaba.

Karin bayani:Dambe: Mayweather ya doke McGregor

Wannan dai ita ce fafatawa ta biyu da Francis Ngannou ke yi a fagen damben, bayan barin wadda ya yi fice a cikinta wato MMA da ake amfani da hannu da kafa wajen duka.

A dambensa na farko dai sauran kiris ya samu nasarar doke zakaran duniya Tyson Furry bayan ya kai shi kasa.