Dambe: Mayweather ya doke McGregor
August 27, 2017Talla
Shahararren dan danben zamani nan dan kasar Amirka Floyd Mayweather ya bige Conor McGregor dan kasar Aylan a karawar da suka yi a birnin Las Vegas na jihar Nevada a gaban 'yan kallo dubu 20 da wasu miliyan dubu a gaban akwatinan Talabijin. Alkali ya tsaida damben ne a zagaye na 10 bayan da McGregor ya kusa ya fita hayyacinsa a sakamakon jerin naushin da ya sha a fuska da ta kai ga kumbirewa.