Tsohon shugaban kasar Faransa Jacques Chirac ya rasu
September 26, 2019Talla
Chirac ya mulki Faransa ne daga shekarar 1995 zuwa 2007, wanda bayan saukarsa daga mulki ya fuskanci zarge-zargen cin hanci da rashawa.
A lokacin mulkinsa, ya kawo sauye-sauye da dama ciki har da rage tsawon wa'adin shugabanci daga shekara 10 zuwa biyar.
Tuni dai shugabannin kasashen duniya ciki kuwa har da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Vladmir Putin na Rasha da Boris Johnson na Birtaniya suka aike da sakonninsu na ta'aziyya ga iyalan Chirac din da gwmanati da al'ummar Faransa.