Tsohon shugaban Iran Rafsandjani ya rasu | Labarai | DW | 08.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon shugaban Iran Rafsandjani ya rasu

Allah ya yi wa tsohon shugaban Iran Ali Akbar Hashemi Rafsandjani rasuwa a wannan Lahadi a sakamakon bugun zuciya.

Kamfanonin dillancin labaran kasar ta Iran na Isna da Fars wadanda suka bayyana labarin mutuwar sun ce tsohon shugaban mai shekaru 82 a duniya ya rasu ne a gidan asibitin Shohadaa na arewacin birnin Teheran inda aka kwatar da shi a yammacin wannan Lahadi bayan da ya samu bugun zuciya. 

Shugaba Rafsandjani wanda ya mulkin kasar ta Iran daga shekara ta 1989 zuwa 1997 ya kasance daga cikin na hannun damar Imam Khomeiny jagoran juyin-juya halin da ya kai ga kafa jamhuriyar musulunci ta Iran a shekara ta 1979. 

Farin jinin Rafsandjani ya ja baya a shekarun baya-bayan nan a fagen siyasar kasar ta Iran. Sai dai duk da haka ya taka muhimmiyar rawa wajen zaben shugaban kasar ta Iran na yanzu mai sassaucin ra'ayi Hassan Rohani a watan Yulin shekara ta 2013 da ma wajen maido da hulda tsakanin kasar da kasanshen Turai kai har ma da Amirka, wacce Iran din ta jima tana yi wa lakabin "Babbar Shedaniya".