Tsohon shugaban Ghana ya rasu | Labarai | DW | 12.11.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon shugaban Ghana ya rasu

Tsohon Shugaban kasar Ghana Jerry John Rawlings ya rasu a wannan Alhamis.

Tsohon janar na soja kuma dan siyasa, Jerry Rawlings ya mulki Kasar Ghana a tsakanin shekarun 1981 zuwa 2001.

Wakiliyarmu ta birnin Accra Jamila Ibrahim Maizango ta shaida mana cewa a wannan Talatar da ta gabata aka kai Mr. Rawlings din asibiti sakamakon wata cuta wacce ba a bayyana ba. A ciki da wajen Ghana ana kallon Jerry Rawlings a matsayin babban jigo wanda ya taimaka wurin hada kan Afirka.