Jerry Rawlings tsohon shugaban kasar Ghana wanda ya karbi madafun iko ta hanyar juyin mulki kafin ya rikide zuwa farar hula.
Ya taka muhimmayar rawa a tarihin kasar ta Ghana da ke yankin yammacin Afirka. Kuma yana cikin mutanen da ake girmamawa a ciki da wajen nahiyar Afirka baki daya.