Tsohon shugaban Chadi Habre zai daukaka kara | Labarai | DW | 09.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon shugaban Chadi Habre zai daukaka kara

Kotu ta musamman da aka girka a Senegal da tallafin Kungiyar Tarayyar Afirka AU, a watan Mayu da ya gabata ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga Shugaba Habre.

Tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre a ranar Litinin din nan zai daukaka kara kan hukuncin da aka yanke masa na daurin rai da rai bisa laifin aikata miyagun laifukan take hakkin bil Adama.

Kotu ta musamman da aka girka a Senegal da tallafin Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU, a watan Mayu da ya gabata ta yanken hukuncin daurin rai da rai ga Shugaba Habre da mulkinsa tsakanin 1982 zuwa 1990 ya zama na 'yan kama karya a kasar ta Chadi, hukuncin da ake gani a matsayin izina ga masu salo na kama karya irin na Shugaba Habre.

Har ila yau kotun a watan Yuli ta nemi tsohon shugaban ya biya kimanin kudi Dala dubu 33,000 ga iyalan kowane daya daga cikin wadanda aka ci zarafinsu ta hanyar fyade ko daurin ba gaira da sauronsu a lokacin mulkin shugaban.

Shugaban dan shekaru 74 ya dai ki amince wa da kotun ta musamman sai dai lauyoyin da aka ba shi a kotun sun nemi daukaka kara a madadinsa.