Tsohon shugaban Brazil zai je gidan kaso | Labarai | DW | 13.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon shugaban Brazil zai je gidan kaso

Shari'ar ta Luiz Inacio Lula da Silva a ranar Laraba ta kasance babbar nasara ga masu aikin binciken badakalar cin hanci.

Tsohon shugaban kasar Brazil da ya sake fitar da sunan kasar a idanun duniya ya samu kai a tsaka mai wuya bayan samunsa da laifi na cin hanci da rashawa da ma badakala ta karkatar da kudaden al'umma, abin da ke nuna cewa a wannan kasa da ke a yankin Latin Amirka aikin binciken cin hanci da rashawa na iya bin kan kowa.

Shari'ar ta Luiz Inacio Lula da Silva a ranar Laraba ta kasance babbar nasara ga masu aikin binciken badakalar cin hanci wadanda tuni suka gabatar da gwamman 'yan kasuwa da 'yan siyasa da ma nasarar karbo sama da Dala miliyan dubu uku na kudaden da aka yi kwana da su.

Tsohon shugaban da ke zama mai karfin fada aji a kasar an yanke masa hukuncin kusan sheklaru 10 a gidan maza, sai dai zai ci gaba da zama cikin 'yanci har sai an ji hukuncin daukaka karar da ya yi.