1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana shari'ar tsohon mashawarcin Macron

Abdul-raheem Hassan
September 13, 2021

Wata kotu a birnin Paris, ta fara shari'ar tsohon mai ba wa Shugaban Faransa Emmanuel Macron shawara kan tsaro Alexandre Benalla, kan zargin cin zarafin masu zanga-zanga a ranar ma'aikata a watan Mayu shekarar 2018.

https://p.dw.com/p/40GTu
Frankreich - Security von Macron - Alexandre Benalla
Hoto: Getty Images/AFP/T. Samson

Shugaba Macron ya sha suka sosai a wancan lokaci, rikicin ya zama na farko da gwamnatinsa ta fara fuskanta tun bayan hawansa mulki. Shari'ar, wacce za ta gudana watanni kadan kafin zaben shugaban kasar Faransa a shekarar 2022, zai nuna allkibla da makomar siyasar Shugaba Macron.

An soki Macron da tawagarsa sosai kan rashin daukar mataki kan mai ba shi shawarar nan take bayan faruwar lamarin, amma daga baya matsin lamba ya sa Macron sallamar Alexander daga aiki bayan wallafa bidiyon abin da ya faru.