Tsipras na cikin tsaka mai wuya | Labarai | DW | 15.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsipras na cikin tsaka mai wuya

Firaministan kasar Girka Alexis Tsipras na ci gaba da fuskantar kalubale daga 'ya'yan jam'iyyarsa ta Syriza gabanin kada kuri'ar amincewa da matakan tsuke bakin aljihu.

Firaministan Girka Alexis Tsipras

Firaministan Girka Alexis Tsipras

Majalisar dokokin kasar ta Girka ce dai za ta kada kuri'ar amincewa da sabbin matakan na tsuke bakin aljihu da gwamnatin Tsipras ta dauka wanda alamu ke nuni da cewa sai dai ya nemi goyon bayan 'yan jam'iyyar adawa kasancewar zai yi wahala 'ya'yan tasa jam'iyyar su kada kuri'ar amincewa. Tuni dai mataimakiyar ministan kudi Nadia Valavani ta ajiye mukaminta, inda ta ce ba za ta iya cin amanar bukatar da al'ummar kasar suka nuna ta yin watsi da matakan tsuke bakin aljihun yayin kuri'ar raba gardama ba. A wani labarin kuma kungiyar kwadagon kasar ta nuna kin amincewarta da matakan na tsuke bakin aljihu da Firaminista Tsipras ya amince da su tare kuma da kiran yajin aiki na tsahon sa'oi 24 a baki dayan ma'aikatun gwamnatin kasar domin nuna adawarta.