1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKenya

Kenya: Tsige mataimakin shugaban kasa

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 1, 2024

Rahotanni daga Kenya na nuni da cewa, wani dan majalisa daga jam'iyya mai mulki ya gabatar da kudirin neman a tsige mataimakin shugaban kasar Rigathi Gachagua daga mukaminsa.

https://p.dw.com/p/4lJDq
Kenya| Mataimakin Shugaban Kasa | Rigathi Gachagua
Mataimakin shugaban kasar Kenya Rigathi GachaguaHoto: LUIS TATO/AFP

Kakakin majalisar wakilan kasar Moses M. Wetang'ula ne ya sanar da hakan, inda ya ce akwai bukatar a tsige Rigathi Gachagua sakamakon yadda yake yin karen tsaye ga kundin tsarin mulkin Kenyan. Ana kuma zarginsa da nuna kaskanci ga gwamnati, baya ga hannu a batun cin-hanci da rashawa da kin yin biyayya ga mahkunta da ma nuna wariya da kabilancin siyasa. Tuni 'yan majalisa 291 suka sanya hannu domin goyon bayan kudirin, abin da ya haura 117 da ake bukata kafin tsige shi. Kakakin majalisar wakilan M. Wetang'ula ya nunar da cewa, kudirin da dan majalisa daga hadakar jam'iyyun da ke mulki a Kenyan Mutuse Eckomas Mwengi ya gabatar ya cika duka ka'idojin da ake bukata.