Tsegerun NDA: Ba mu da niyar kashe kowa | Labarai | DW | 03.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsegerun NDA: Ba mu da niyar kashe kowa

Tsagerun Niger Delta Avengers sun karyata zargin da sojoji suka yi musu na yunkurin kitsa kai hari a kan babban jami'in tsaro da fasa bututun man fetur.

Tsagerun yankin Niger-Delta na tarayyar najeriya sun yi fatali da zargin da aka yi musu na kitsa manakisar halaka wani babban jami'in tsaro a Arewacin kasar. A ranar Jumma'a ce dai hukumar tsaro ta faran kaya ta kama wasu 'yan kungiyar Niger Delta Avengers bisa zarginsu da yunkurin kai hari a Kaduna don kashe wani hapsan soji, da kuma fasa bututun man fetur.

Sai dai a lokacin da ya mayar martani, kakakin NDA Mudoch Agbinibo ya ce wadannan zarge-zargen ba su da tushe da kuma makama. Sannan ya kara da cewa duk wadanda aka kama 'yan kora ne na hukumar leken asirin Najeriya.

Su dai tsagerun kungiyar NDA da suka bayyana a watan Mayun wannan shekarar, sun bayyana burinsu na samar da 'yantaciyyar kasar Biafra. Sannan kamar sauran tsagerun, sun nunar da cewar yankin Niger Delta ba ya cin gajiya yadda ya kamata na arzikin man fetur da Allah ya hore masa.