Tsawaita zaman sojojin Jamus Mali | Siyasa | DW | 20.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tsawaita zaman sojojin Jamus Mali

Bisa ga dukkan alamu hukumomi a Jamus, sun gamsu da aikin da sojojin kasar ke yi na bada horo wa rundunar sojan kasar Mali, wanda ke gudana bisa jagorancin ƙungiyar EU

Majalisar dokokin da kuma gwamnatin ƙasar ta Jamus kan ta, na duba yiwuwar ƙara wa'adin aikin sojojin ƙasar cikin rundunar ƙasashen Tarayyar Turai a Mali, har izuwa nan da shekara guda. Kimanin sojojin ƙasar Jamus 250, za su kasance cikin aikin na wazar da zaman lafiya a ƙasar da ke yammacin Afirka. Babban ayyukan da sojojin Jamus ke yi, sun haɗa da horar da sojojin ƙasar ta Mali da kuma bada tallafin magani. An dai tura dakarun kiyaye zaman lafiya a Mali, bayan tashin hankali da ya rutsa da ƙasar.

Sansanin horar da sojojin Mali da ke birnin Kolikoro, wanda tafiyar kimanin sa'a guda ne a mota daga Bamako, babban birnin ƙasar ta Mali. Su ma dai kansu sojojin na Tarayyar Turai da ke bai wa na Mali horo, dole suna kula da tsaron lafiyarsu a ƙasar, domin gudun farmaki daga ƙungiyoyin 'yan ta'adda, misali ƙasar Faransa da ta jagoranci farmaki a ƙasar ta Mali, yanzu ta shirya janye dakarunta kimanin 1000. Domin kuwa masu kaifin kishin Islama sun kai wa kamfanoni mallakar ƙasar ta Faransa hari, har cikin ƙasar Nijar bisa abinda suka ƙira daukar fansa. Ana saran sojojin Mali za su maye gurbin dakarun na Faransa a cewa Nouhou Traore, wanda tsohon dalibi ne a Hamburg, yanzu kuma ke tare da sojojin Jamus.

"Aikin da sojojin Jamus ke yi a nan yana da matuƙar mahimmanci. Ba tare da taimakon sojojin Jamus ba, da babu wani soja ɗan ƙasar Mali a nan"

Ana dai buƙatar aiki tuƙuru domin sake farfaɗo da rundunar sojan Mali, inda a bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekara ta 2012, mayaƙa masu kaifin kishin Islama suka fatattaki sojojin Mali daga arewacin ƙasar, abinda ya haifar da ruɗanin tsaro a ƙasar. Yanzu haka an horar da kimanin bataliya huɗu, wato ksusan sojoji 2500. To amma kakakin rundunar sojan kasar Mali Souleymane Maiga, ya yi farin cikin jin ƙasar Jamus za ta tura ƙarin dakaru, masu bai wa sojan Mali horo.

"Manufar sojojin mu shi ita ce, haɗa kan ƙasa da kuma bada tsaro a ɗaukacin ƙasar Mali. Muna son shiga yaƙin sake haɗewar ƙasa, don haka muke ta ɗaukar sabbin mutane aikin soja. To amma idan muna da sojojin, muna kuma buƙatar ƙwararrun sojojin Mali, don haka dole mu samu aci gaba da aiki da rundunar bada horon soja"

A farkon watan nanne ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen, ta kai ziyara a sansanin da sojojin na Jamus ke bada horo a ƙasar ta Mali, domin ganewa kanta aikin da su ke gudanarwa. A ziyarta, ministar tsaro Leyen ta fadi ƙarara, sojojin Jamus ba za su taɓa shiga fagen daga ba a Mali, amma za su ci gaba da kasancewa masu bada horo ƙarƙashin MDD. Inda ta ce.

"Ko wane tashin hankali da yadda yake faruwa, Idan aƙarƙashin MDD, ko kuma ƙarƙashin Tarayyar Turai, to in abu ya shafi rundunar da ke ƙarƙashin tarayyar Turai to an son irin matsayinmu, idan kuma ƙarƙashin MDD ma haka"

Wannan dai ya nuna cewa, Jamus a shirye ta ke don yin aiki da ƙawayenta musamman ƙasar Faransa wajen kawo zaman lafiya. Don haka mahawarar da hukumomi ke yi kan rundunar sojan ƙasar, ba wai ga ƙasar Mali kawai ba, amma har izuwa wasu ƙasashen da ke nahiyar Afirka idan hakan ta taso.

Mawallafa: Alexander Göbel / Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin