Tsananin boren neman murabus na Zuma | Labarai | DW | 07.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsananin boren neman murabus na Zuma

Masu zanga-zanga sun mamaye biranen Afirka ta Kudu inda suke kiraye-kirayen saukar shugaban kasar daga mulki.

Sama da mutane dubu 30 ne suka yi zanga-zanga a kasar Afirka ta Kudu a wannan Juma'a, inda suke kiran shugaba Jacob Zuma na kasar da ya yi murabus.

Dubban masu boren da suka bazu a manyan garuruwan kasar, na kiran saukar shugaba Zuman ne bayan garanbawul da shugaban ya yi a majalisar ministocin kasar. Bayanai sun ce 'yan sandan kasar na amfani da albarusan roba da kuma barkonon tsohuwa kan wasu 'yan jam'iyar ANC a birnin Johannesburg, wadanda ke kokarin nuna fushi kan 'yan adawar kasar, ta hanyar afka masu.

Matakin sallamar ministan kudin kasar cikin garambawul da shugaba Zuma ya yi a ranar Alhamis na makon jiya, ya tayar da jijiyoyin wuya a kasar, ciki kuwa har da 'ya'yan jam'iyyar ANC mai mulki tun cikin shekara ta 1994 bayan mulkin farar fatan kasar.