Tsaka mai wuya ga Musulmin Bama | Labarai | DW | 15.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsaka mai wuya ga Musulmin Bama

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya ce ya damu matuka da rahotanni da ke nuni da cewa wasu kasashe sun hana daruruwan 'yan gudun hijirar Bama shiga kasashensu.

Halin da Musulmin Rohingya da ke gudun hijira ke ciki

Halin da Musulmin Rohingya da ke gudun hijira ke ciki

Sama da Musulmin Rohingya da ke gudun hijira da ga kasar ta Bama 1,000 da suka tserewa kashe su da mabiya addinin Buda ke yi a kasarsu ne ke cikin halin tasku da ya hadar da yunwa da kishirwa da kuma rashin koshin lafiya ke neman mafaka, inda rahotanni ke nuni da cewa kasar Bangaladash da sauran kasashen yankin kudancin Asiya sun koresu tare da hanasu shiga kasarsu. Ban ya bukaci gwamnatocin yankin kudancin na Asiya da su bar tashoshin jiragen ruwansu a bude kana su basu damar shiga domin samun taimakon gaggawa da suke bukata.