Tsagaita wuta a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 11.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsagaita wuta a Sudan ta Kudu

Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir ya sanar da tsagaita wuta tsakanin dakarunsa da bangaren mataimakinsa Riek Machar bayan kiraye-kiraye daga al'ummomin kasa da kasa.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da sakatere janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya kirayi dukkanin bangarorin da ke yakar juna a kasar da su gaggauta kira ga magoya bayansu, kan su ajiye makamai ko su fuskanci hukuncin mai tsanani. Ban ya kuma bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar da ya dau mataki a kan duk wadanda aka samu da hannu cikin yunkurin tada zaune tsaye. A wannan Litinin din kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniyar ya shawo kan dakarun da ke biyayya ga shugaban kasar Salva Kiir da kuma na bangaren mataimakinsa kana jagoran 'yan tawayen kasar Riek Machar a wani yunkuri na kawo karshen luguden wuta da suke wa juna na tsahon kwanaki hudu, wanda kuma ya yi sanadiyar asarar rayuka kusan 300.