1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a jibge jami'an tsaro a biranen Amirka

July 23, 2020

Shugaba Donald Trump na Amirka ya ce zai jibge daruruwan jami'an tsaro a manyan biranen kasar.

https://p.dw.com/p/3foxu
USA Präsident Trump
Hoto: Reuters/L. Millis

Trump na fatan jami'an tsaron su murkushe wadanda ya ce ke ci gaba da kawo tarnaki ga zaman lumanar Amirka.  Bill Barr, Antoni-Janar na kasar ya ce za su tura 'yan sanda 200 zuwa Chicago da kuma wasu jihohi na kasar. 

To sai dai da take mayar da martani kan wannan mataki, magajin garin birnin Chicago Lori Lightfoot  ta soki yunkurin, ta kuma lashi takobin cewa ba za ta bar Shugaba Donald Trump ya turo ma ta jami'an tsaro da za su rikita jama'a ba. 

Abubuwa dai sun fara rinca'bewa a Amirka tun bayan kisan da wani dan sanda farar fata ya yi wa wani bakar fata, lamarin da ya janyo zanga-zanga wace ta rikide ta koma tashin hankali.