Trump na adawa da dokar zama dan kasa ta haihuwa
October 31, 2018Talla
A wani mataki na jaddada manufar yaki da shigowar 'yan ci rani Amirka, Shugaba Donald Trump ya ce doka ta ba shi damar soke duk wasu damarmaki da jarirai ke samu bayan an shigo da su da ciki zuwa Amirka, ciki har da mallakar takardar izinin zama dan kasa na shekaru 85.
Shugaba Trump ya ce Amirka ce kadai ke amfani da wannan tsarin a yanzu, yayin da a kasashe da dama dokar ta zama tsohon yayi.
Trump na ci gaba da tsaurara matakan dakile kwararar bakin haure a matsayin jigon yakin neman zabe, inda ya ce matakan ba su da barazana ga zaben tsakiyar zango da za a shiga nan ba da jimawa ba.