Amirka da Guatemala sun cimma yarjejeniya
July 27, 2019Shugaban Amirka Donald Trump ya sanar da cewa kasarsa ta cimma yarjejeniya da Guatemala yayin da Amirka ke kokarin dakile matsin lambar da ta ke fuskanta na kwararar 'yan gudun hijira a kudancin iyakar kasar.
“Ya ce wannan lamari ne babba, yarjejeniya ce mai muhimmanci wadda ba a taba yin irinta ba a baya.”
Trump ya ce yarjejeniyar za ta kare hakkin wadanda ke da kwararan hujjoji na shiga Amirka yayin da a waje guda kuma za ta kawo karshen keta tsarin neman mafaka da kuma sassauta matsaloli a kudancin iyakokin Amirka.
Wannan dai na zuwa ne yan kwanaki bayan da Trump ya yi barazanar kakaba wa kasar ta Guatemala takunkumi idan ta ki rattaba hannu a kan yarjejeniyar.
Mukaddashin sakataren tsaron cikin gida na Amirka Kevin McAleen ya shaidawa yan jarida cewa tsarin zai bada kariya ga masu neman mafaka daga masu safarar mutane ta haramtacciyar hanya.
Fadar white House ta ce masu neman mafakar za su tsaya ne a Guatemala inda daga nan ne za su mika takardar su ta neman mafaka a Amirka.