Trump: Ya zabi Pence a matsayin mataimaki | Labarai | DW | 15.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump: Ya zabi Pence a matsayin mataimaki

Dan takarar jam'iyyar Republican a zaben shugaban kasar Amirka Donald Trump ya zabi gwamnan jihar Indiana Mike Pence a matsayin mataimakinsa a zaben 2016.

A cikin sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ne Trump ya sanar cewa ya zabi Mike Pence a matsayin mataimaki. Zai jadadda wannan sanarwa a wani taron manaima labarai da zai gudanar a ranar Asabar.

Shi dai gwamna Mike Pence ya na da tsattsauran ra'ayi kan lamarun da suka shafi zubar da ciki. Sai dai zai iya taimaka wa Donald Trump samun karbuwa tsakanin 'yan jam'iyyar Conservative da ke adawa da manufofinsa.

A cikin mako mai zuwa ne dai jam'iyyar Republican za ta gudanar da babban taronta domin tsayar da Donald Trump a hukumance a matsayin dan takara. Zai fafata da Hilary Clinton 'yan takarar Democrat a zaben shugaban kasar Amirka da zai gudana a ranar 8 ga watan Nowamba na 2016.