Trump ya soki tsarin tattalin arzikin Japan | Labarai | DW | 25.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ya soki tsarin tattalin arzikin Japan

Shugaban kasar Amirka ya nemi Japan ta sauya tsarin kasuwanci

Daga isar Trump a Tokyo nan take ya shiga zauren ganawa da 'yan kasuwan kasar ta Japan, inda Trump ya nemi 'yan kasuwan Japan da su zuba wadataccen jari a kasuwannin Amirka. Shugaban kasar ta Amirka ya bayyana cewa yunkurinsu na sasantawa kan dokokin kasuwancin Japan ya gamu da turjiya, a wasu lokutanma har tattaunawar ta yi kusan ta watse. Daga cikin shugabannin kamfanonin da Trump ya gana da su, sun hada shugaban kamfanin motocin Hunda da na Toyota da kuma shugaban kamfanin Nissan gami da shugabannin man'yan bankunan kasar.