Trump ya bukaci a hana Musulmai shiga Amirka | Labarai | DW | 08.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ya bukaci a hana Musulmai shiga Amirka

Wannan kalamai dai na dan takarar shugabancin kasar ta Amirka Trump na zuwa ne mako guda bayan harin da aka kai a San Bernardino.

USA Präsidentschaftswahl Kanditat der Republikaner Donald Trump

Donald Trump

Dantakarar shugabancin kasar Amirka karkashin jam'iyar Republican Donald Trump ya yi kira da a hana duk wani Musulmi shiga Amirka a halin yanzu.

Wannan kalamai dai na Trump na neman hana shigar baki Musulmi kasar ta Amirka ya jawo suka daga dukkanin bangarori na siyasar kasar ciki kuwa har da abokin takararsa daga jam'iyyar ta Republican Jeb Bush wanda ya bayyana shi da zama mai firta kalamai ba tare da tunani ba. Shi dai wannan dan takara na zuwa da kalamai da ke sanyawa a tada jijiyar wuya amma duk da haka yana kara samun magoya baya.

Wannan kalamai dai na wannan dan takarar shugabancin kasar ta Amirka Trump na zuwa ne mako guda bayan harin da aka kai a San Bernardino wanda hukumar binciken manyan laifuka a Amirka FBI ta ce ma'auratan biyu da suka kai harin sun sauya daga masu sassaucin ra'ayi zuwa masu tsatstsauran ra'ayi na addinin Islama, dalilan da ya sa ya ce adaina barin Musulmi shiga kasar har sai an lamura sun daidaita. Har ila yau kalaman na zuwa ne kwana daya bayan da shugaban kasar ta Amirka Barrack Obama ya yi jawaban Allah tsine kan ayyukan ta'addanci.