1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya amince da takara a wa'adi na biyu

August 28, 2020

Shugaban Amirka Donald Trump ya karbi amincin takarar shugabancin kasar a karo na biyu da jam’iyyarsa ta Republican ta yi masa a karshen babban taron jam’iyyar na kasa.

https://p.dw.com/p/3hcQF
USA Nominierungsparteitag der Republikaner
Hoto: picture-alliance/RNC/J. Koscielniak

Da yake jawabi a fadar White House, Trump yace ya amince zai tsaya takara, yana mai jaddada yabo da godiya a zuciyarsa da kuma kwakkwarar kudiri na yiwa kasa aiki. Ya baiyana zaben da ke tafe a matsayin mafi muhimmanci a tarihin Amirka.

Trump ya soki abokin hamaiyarsa na jam’iyyar Democrat Joe Biden wanda ya baiyana da cewa bai taba zama zabi mafi dacewa a tsakanin jam’iyyu biyu ko tafarki guda biyu ba. 

Shugaban ya kuma baiyana manufofin jam’iyyar Democrat a matsayin mafi tsaurin ra’ayi da wata babbar jam’iyya ta taba gabatarwa.