1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

FBI zata kaddamar da bincike kan Kavanaugh

Zainab Mohammed Abubakar
September 29, 2018

Shugaban Amurka Donald Trump ya umurci hukumar binciken kasar ta FBI da ta sake gudanar da sabon bincike kan zargin cin zarafi ta hanyar lalata da ake wa mutumin da ya ke shirin bai wa kujerar kotun kolin kasar.

https://p.dw.com/p/35gmH
Brett Kavanaugh Anhörung vor dem US-Senat wegen Missbrauchsvorwürfen
Hoto: Reuters/M. McClain

'Yan majalisar dattijai dai sun jinkirta kada kuri'ar tabbatar da Brett Kavanaugh, a wani mataki na bada damar kammala bincike a kansa kafin ya hau wannan mukami.

Bayan sauraron bahasin wata farfesar jami'a da ke zargin shi da cin zarafinta a wajen wata liyafa a shekarun 1980s, kwamitin kula da harkokin shari'a na majalisar dattijai ya amince da nadin nasa, a kwarya-kwaryar kuri'a da 'yan majalisar suka kada.

Sai dai bayan matsin lamba daga ciki da wajen majalisar, shugaban kwamitin kuma dan jam'iyyar Republican Chuck Grassley ya sanar da cewar zai nemi shugaba Trump ya sake kaddamar da bincike kan zargin da ake wa Brett Kavanaugh. Kuma kada sakamakon binciken ya shige nan da mako guda.