Trump na shan suka kan bukatar dage zabe
July 31, 2020Talla
Trump ya fuskanci kakkausar suka daga 'yan jam'iyyarsa ta Republican da kuma 'yan jam'iyyar adawa ta Demokrat a majalisar dokoki yayin da wasu ke cewa kiran dage zaben wani yunkuri ne na kawar da hankulan jama'a daga koma bayan tattalin arziki da kasar ke fuskanta.
Sai dai kuma da yake jawabi ga manema labarai a fadar White House Trump yace ya bukaci jinkirta zaben ne saboda baya so a sami nakasu saboda annobar corona.
"Yace bana so na ga zabe wanda za a ce ana hasashen waye ya yi nasara bayan sati daya ko wata daya da ma shari'a wadda mai yiwuwa za ta dauki tsawon lokaci ana yi ko ma watakila a rasa sanin wanda ya lashe zaben".