1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump na karbar bakoncin Firaministan Italiya

Mohammad Nasiru Awal AS
July 30, 2018

Wannan ita ce ziyarar ta farko da Giuseppe Conte ya kai fadar White House. Sau da yawa Trump na nuna kamanceceniya tsakaninshi da Conte.

https://p.dw.com/p/32Lev
USA Washington Donald Trump & Giuseppe Conte, Ministerpräsident Italien
Hoto: Reuters/B. Snyder

Shugaban Amirka Donald Trump na karbar bakoncin Firaministan Italiya Giuseppe Conte a fadar White House, inda ake sa ran shugabannin biyu za su tattauna kan huldar dangantaku tsakanin kasashensu.

Wannan shi ne karo na farko da Firaministan na Italiya ya kai ziyara a fadar White House. Sau da yawa an ji Trump na nuna kamanceceniya tsakaninshi da Firaministan na Italiya musamman dangane da batun bakin haure.

A ganawa da manema labarai kafin sun kebe zauren tattaunawa, Trump cewa ya yi.

"Ina godiya da zuwanka nan. Mun zama abokai tun a tarukan G7. Na amince kana tafiyar da aiki mai kyau musamman dangane da masu kaura da bakin haure. Italiya na daukar matakan da suka dace a kan iyakokinta, matakin da wasu daidaikun kasashe suka riga suka dauka."

Taron dai na zuwa ne bayan da a ranar Lahadi Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa a shirye yake ya rufe dukkan ma'aikatun gwamnati idan 'yan jam'iyaar Demokrats suka ki jefa kuri'a kan kare iyakokin Amirka ciki har da batun gina katanga tsakaninta da Mexiko.