Trump: Kishiya ga kafafen sada zumunta | Labarai | DW | 22.02.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump: Kishiya ga kafafen sada zumunta

Tsohon shugaban kasar Amirka Donald Trump ya kaddamar da sabon shafinsa na sada zumunta, wanda ya yi wa lakabi da "Truth Social" tare da samar da shi a kan manhajar nan ta Apple's App store.

Trump ya kaddamar da shafinsa na „Truth Social“

Tsohon shugaban kasar Amirka Donald Trump

Wani daga cikin ma'aikatan shafin na "Truth Social," ya nunar da cewa ana sa ran shafin zai fara aiki ka'in da na'in a karshen watan Maris mai zuwa. Shafukan sada zumunta na zamani da suka hadar da YouTube da Twitter da kuma Facebook, sun dakatar da Trump har na tsawon sama da shekara guda biyo bayan harin da magoya bayansa suka kai a ginin majalisar dokokin Amirka na Capitol a ranar shida ga watan Janairun bara. Trump wanda ya bayyana cewa sabon shafin nasa zai bayar da damar 'yancin fadar albarkacin baki, an zarge shi da tunzura magoya bayan nasa da suka kai harin na Capitol.