Trump da Kim Jong Un sun yi musabaha | Labarai | DW | 30.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump da Kim Jong Un sun yi musabaha

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un da takwaransa Donald Trump na Amirka sun hadu don yin hannu da hannu kamar yadda shugaba Donald Trump ya bukata a wani yanki da ke tsakanin Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu.

A yayin taron manyan kasashen duniya mafi karfin tattalin arziki da ya gudana a kasar Japan ne shugaba Donald Trump ya gayyaci takwaransa na Koriya ta Arewa a shafinsa na Twitter, inda ya bukaci su hadu don su yi hannu da hannu. Rahotanni sun nunar da cewa  tun da farko cewa shugabannin biyu sun yi ganawar ne a gaban takwaransu na kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-in.

Shugaban Amirka Donald Trump shi ne ya fara sauka tun da sanyin safiyar wannan Lahadi a yankin da ba ya da ayyukan soja tsakanin Koriyoyin guda biyu, kafin daga bisani takwaransa Kim Jong Un ya tarar da shi, kana kuma Trump ya ce ban hannun da yayi da Kim na cike da tarihi.