Togo: Za ta shiga Commonwealth | Labarai | DW | 27.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Togo: Za ta shiga Commonwealth

Gwamnatin kasar Togo na ci gaba da yin wani yunkurin diplomasiya don ganin kasar ta shiga cikin kungiyar kasashe raino Ingila watau Commonwealth.

Togo wacce Faransa ta yi wa mulkin mallaka mai yawan al'umma milyan bakwai ta soma tattaunawar shiga cikin kungiyar ce ta Commonwealth tun a shekara ta 2014. Tuni dai da babbar jam'iyyar adawa ta kasar watau ANC ta yi Allah dai da yunkuri gwamnatin na shiga cikin kungiyar wanda ta ce wani abin dariya ne ga kasashen duniya wanda kuma ba shi da digi.