Togo: Bude taron AGOA karo na 16 a Lome | Labarai | DW | 09.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Togo: Bude taron AGOA karo na 16 a Lome

Birnin Lome na kasar Togo ya karbi babban zaman taron tsarin bunkasa da kuma hanyoyin karfafa tattalin arzikin Afirka na AGOA karo na 16 wanda Firaministan na Togo ya jagoranci budawa.

Taron ya samu halartar wakillan kasashe 38 na Afirka kudu da Sahara mambobi a wannan tsari na AGOA, tare da 'yan kasuwa na kasar Amirka. Taken taron na bana shi ne "Amirka da Afirka" hulda da cigaba ta hanyar kasuwanci. Cikin wani sako da ya aike wa mahalarta taron, Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé, ya yi kira ga mahalarta taron da su yi nazari mai zurfi ta yadda za a samu kari a kayayakin da kasashen na Afirka ke fitarwa wanda yawan su ya ja baya a 'yan shekarun baya-bayan nan. 

Shugaba Gnassingbé ya kara da cewa har ya zuwa yanzu kasashen na Afirka ba su kai ga cin moriyar da ta kamata a ce sun yi kan damar da wannan tsari na AGOA ke bayarwa ba. A shekara ta 2000 ne dai tsohon Shugaban Amirka Bill Clinton ya kafa wannan tsari na AGOA domin bai wa 'yan Afirka damar fitar da kayayakinsu zuwa Amirka ba tare da biyan kudaden fito ba.