Togo: An kashe mutane biyar | Labarai | DW | 19.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Togo: An kashe mutane biyar

Arangama tsakanin masu zanga-zangar nuna adawa da Shugaba Faure na kasar Togo ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar a cewar ministan tsaron kasar ta Togo Yark Damehane.

Uku daga cikin mutanen biyar sun mutu ne sakamakon harbinsu da bindiga a birnin Sokode birni na biyu mafi girma a kasar a cewar ministan yayin wani taron manema labarai da ya jagoranta. Ministan tsaron na Togo ya kara da cewa wani kuma daga cikin masu zanga-zangar ya mutu  a Lome babban birnin kasar, sai dai kuma 'yan adawar sun ce mutun biyu ne suka mutu a birnin na Lome kadai cikinsu kuwa har da wani yaro dan shekara 11 da haihuwa. Masu zanga-zangar dai sun kafa shingaye a titunan biranen kasar, inda suka sha alwashin cigaba da zanga-zangar har sai sun ga bayan mulkin gado na iyallan gidan Gnassingbe, ko kuma a dawo da kudin tsarin mulkin kasar na 1992.