1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Theresa May na fafutukar kare Brexit

Yusuf Bala Nayaya MNA
December 10, 2018

Firaministar Birtaniya Theresa May ta tsara ganawa da 'yan majalisa na jam'iyyarta a wannan Litinin a kokari da take yi na neman goyon baya kan shirinta na janye Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai.

https://p.dw.com/p/39npj
Großbritannien Parteitag Conservative Party | tanzende Theresa May, Premierministerin
Hoto: Getty Images/J.J. Mitchell

Kafar yada labaran kasar ta Birtaniya (BBC) ta ce May za ta zauna tattaunawa ta sirri da 'yan majalisa, mambobin jam'iyyarta bayan da dama masu goyon bayan ci gaba da kasancewar a Tarayyar Turai da wasu da ba sa goyon baya suka sha alwashi na kin mara baya ga May, lamarin da ya jefa yunkurin firaministar cikin halin kila-wa-kala. Abin da ke nufin ya zame mata dole ta shawo kan 'yan majalisar da suka yi mata tawaye muddin tana so ta kai labari.

Har ila yu kamar yadda  wasu kafafan yada labaran a Birtaniya kamar Financial Times da sauransu suka nunar da cewa wata kila May na iya tsayar da shirin kada kuri'ar da za a yi a ranar Talata muddin ta gaza shawo kan 'yan majalisar da take neman goyon bayansu, ya zuwa yanzu rahotanni sun nunar da cewa ta dage zaman kada kuri'ar na ranar Talata.