1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Tawagar MDD na kan hanyar zuwa gabashin Kwango

Abdoulaye Mamane Amadou
February 3, 2026

Kwana guda bayan soma tattaunawa kan batun zaman lafiya a gabashin Kwango, Quatar dake shiga tsakani ta tabbatar da cewar wata tawaga ta Majalisar Dinkin Duniya za ta isa a yankin nan ba da jimawa ba.

https://p.dw.com/p/57zSF
Hoto: Mahmud Hams/AFP

Majalisar Dinkin Duniya za ta tura tawaga nan da 'yan kwanaki masu a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango, da nufin fara aikin tabbatar da tsagaita wuta a yankin, duk da ci gaba da rikice-rikicen da ake samu a yankin a baya-bayan nan.

Kwango: Mutane 200 sun mutu a ruftawar mahakar ma'adanai

Gwamnatin Qatar da ke jagorantar tattaunawar sulhu tsakanin Kwango da kungiyar M23 ce ta sanar da matakin a wannan Talata, kwana guda bayan wani sabon zama da ake gudanarwa a Doha tsakanin wakilan M23 da jami'an gwamnatin Kinshasa.

Kwango ta zargi Ruwanda da kashe daruruwan fararen hula

Qatar ta tabbatar da cewa bangarorin biyu sun amince da yadda za a kafa tsarin, wanda ake sa ran rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya Monusco za ta yi ruwa da tsaki wajen aiwatar da tsarin, inda za ta fara aikin sa idon da tsagaita wuta a birnin Uvira, wani muhimmin birni na kasar Kwango mai iyaka da Burundi.

Mayakan sa kai sun kashe mutane sama da 20 a Kwango

A farkon watan Disamban bara, birnin Uvira ya fada hannun M23, kafin daga bisani dakarun kungiyar su janye, lamarin da ya bai wa rundunar sojin Kwango damar sake karbe birnin.