Taurarin da za su haska a gasar AFCON
Gasar cin kofin Afrika za ta gudana daga ranar 9 ga Janairu zuwa 6 ga Fabrairu 2022 a Kamaru. Ana ganin cewar wasu manyan 'yan kwallon za su taka rawar gani tare da neman cire wa kasashensu kitse a wuta.
Mohamed Salah - Masar
Mohamed Salah yana kan aniyarsa ta kwallon kafa a kulob dinsa na Liverpool a Ingila. Ya kasance a matsayi na bakwai a gasar Ballon d'Or ta 2021. Ya lashe kyautar Ballon d'Or ta Afirka a 2017 da 2021. Burinsa shi ne ya samar wa Masar kofin nahiyar Afirka karo na takwas a tarihinta.
Edouard Mendy - Senegal
Edouard Mendy ya zama wanda ake ji da shi a Chelsea tun bayan zuwansa daga Stade Rennais a 2020. Tare da Blues, ya lashe gasar zakarun kasashen Turai a 2021. Yana daya daga cikin manyan masu tsaron gida a duniya. Don haka dan Senegal din zai zama katanga ga kungiyar Lions de la Teranga.
Amadou Haidara - Mali
A matsayinsa na mai shekaru 24, Amadou Haidara ya zama ginshiki ga kulob din RB Leipzig na Jamus. Har ila yau, shi ne babban dan wasan tsakiya na Aigle du Mali, wacce ba a jin za ta taka rawar gani a gasar AFCON ta 2022.
Karl Toko-Ekambi - Kamaru
Karl Toko-Ekambi yana karyawa inda ba gaba a Olympique Lyonnais. Shi ne ya zura kwallon da ta bai wa Kamaru damar shiga gasar cin kofin duniya a shekarar 2022. Saurinsa ya ba shi matsayi na musamman a cikin kungiyar Indomitable Lions. Shi ne zai kasance babban dan wasan gaba na kungiyar.
Edmond Tapsoba - Burkina Faso
Duk da raunin da ya yi wanda ya hana shi shiga fili na tsawon watanni, dan wasan Bayer Leverkusen yana daya daga cikin 'yan wasan baya da ake nema ruwa a jallo a Turai. Edmond Tapsoba ne jagoran tsaron Burkina Faso, wanda zai yi duk abin da ya dace don cimma kyakkyawan matsayi kamar a 2013.
Franck Kessié - Côte d'ivoire
Franck Kessié ne jagoran 'yan wasan tsakiya na Côte d' Ivoire. Har ila yau, muhimmin dan wasa na AC Milan, kulob dinsa tun 2017. Likimonsa da hangen nesansa game da wasa sun zama madogara ga Côte d' Ivoire.
Kamaldeen Sulemana - Ghana
Dan wasan na Ghana na cikin bayyana baiwarsa ga kasashen Turai. Kungiyoyin Turai da dama na bibiyar wanda ke yi wa Rennes wasa. Karfinsa da saurinsa da salon taba kwallonsa za su kawo ci-gaba ga Ghana, da ke neman sake kaiwa matkin kusa da karshe na AFCON.
Eric Maxim Choupo-Moting
Choupo-Moting ya zama jagoran tawagar kwallon kafar Kamaru. Duk da karancin lokacin wasa tare da Bayern Munich, amma dan wasan ya kasance mai mahimmanci a cikin kungiyar Indomitable Lions. Yana da shekaru 32, kuma zai kasance daya daga cikin gogaggun 'yan wasan Kamaru..
Sébastien Haller - Côte d'ivoire
Mahimmancinsa a Ajax Amsterdam a wannan kakar, musamman a gasar zakarun Turai inda yake fafatawa da manyan 'yan wasan gaba, Sébastien Haller ne zai jagoranci masu kai hari na Côte d' Ivoire. Tsohon dan wasan Frankfurt ya samu matsayi a Côte d' Ivoire a shekarar 2020.
Riyad Mahrez - Aljeriya
Kyaftin na tawagar Aljeriya mai rike da kofin nahiyar Afirka, Ana jiran Riyad Mahrez a kwana a lokacin wannan AFCON ko CAN. Duk da rashin gamsuwa da rawar da ya taka a wasan watannin baya, amma magoya bayan Aljeriya suna tsammanin cewa zai iya taka rawar gani kamar a kulob dinsa na Manchester City. Burin wanda ya ci Ballon d'Or na Afirka ta 2016 shi ne lashe kofin.
Islam Slimani - Aljeriya
Har yanzu Islam Slimani yana cikin jerin 'yan wasan Aljeriya. Duk da matsayinsa na mai maye gurbinsa a kungiyar Olympique Lyonnais, zai kasance daya daga cikin ginshikan kasar Aljeriya. Djamel Belmadi ya san cewa koyaushe zai iya dogara a kan dan wasansa, wanda ya fi kowa zura kwallaye a tarihin kasar wato kwallaye 38.
Sadio Mané - Senegal
Jigon a tawagar 'yan kwallon Liverpool ta Jürgen Klopp, Sadio Mane yana daya daga cikin mafi zakakuran 'yan wasan gaba a duniya. Kyaftin na kungiyarsa, shi ne babban ginshikii na Lions de la Terranga. Bayan gasannin AFCON biyu da Senegal ba ta gurbe ba, a ƙarshe yana so ya jagoranci abokan wasansa zuwa nasara a wannan karon.