Tattaunawar sulhu kan makomar Yemen | Labarai | DW | 15.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawar sulhu kan makomar Yemen

Babban kalubale shi ne ya zaman na Geneva zai kasance bisa jagorancin Majalisar Dinkin Duniya za a zauna wuri guda ne tsakanin bangaren gwamnati da 'yan tawaye ko kuwa.

Jemen Politiker auf dem Weg nach Genf

Tawagar masu ruwa da tsaki a rikicin Yemen

Bangarori biyu masu gaba da juna a kasar Yemen za su taru a karon farko a Geneva a ranar Litinin din nan a kokarin kawo karshen zubar da jini a fafatawar da a ke yi tsakanin bangaren Houthi da ke zama 'yan Shi'a masu samun goyon bayan kasar Iran, da sojoji da ke mara baya ga gwamnatin Abedrabbo Mansour Hadi.


Jakadan Majalisar Dinkin Duniya da ke shiga tsakani a shirin na sulhu Ismail Ould Cheikh Ahmed ya ce za su ga yadda fara wannan tattaunawa za ta yi tasiri wajen kawo karshen yaki da ya jawo kisan fiye da mutane 2,500, abin da ya bude kofa ga shirin neman agajin kasa da kasa ga dubban al'umma da yaki ya ritsa da su.

A cewar wasu masharhanta dai da wuya a wannan tattaunawa a cimma wata nasara kasancewar tawagogin ba ma za su zauna bane wuri guda dan fahimtar juna.