Tattaunawa kan warware rikicin Gaza | Labarai | DW | 25.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawa kan warware rikicin Gaza

Nan gaba kadan ne majalisar ministocin Izra'ila za ta yi tattaunawa kan wani kudurin samar da zaman lafiya tsakanin Izra'ilan da Hamas wanda suka kwashe makonni suna rikici.

Wannan zama da za a yi dai shi ne sabon yunkuri na baya-bayanan nan na ganin an kawo karshen zub da jinin da ake yi tsakanin bangarorin biyu wanda ya yi sanadiyar rasuwa falasdinawa kimanin 800 da sojin Izra'ila sama da 30.

Hakan dai na zuwa ne bayan da a jiya Alhamis wani farmaki da dakarun Izra'ila suka kai wani sansani na Majalisar Dinkin Duniya inda falasdinawa da dama ke samun mafaka ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama, lamarin da ya jawo maida martani kakkausa kan sojin Izra'ila daga sassa daban-daban na duniya.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu